Isa ga babban shafi
Yankin Sahel

Sahel: Amurka da Faransa sun amince da kafa runduna ta musamman

Amurka da Faransa sun amince da daftarin da zai bukaci kafa runduna ta musamman, da zata kunshi sojoji 5,000 daga kasashe biyar na yankin Sahel, domin murkushe hare-haren ta’addancin da ke karuwa a yankin.

Dakarun Mali da aka girke a wurin shakatawa na Kangaba, da ke wajen birnin Bamako, bayan harin da kungiyoyi masu da'awar jihadi suka kai wurin..
Dakarun Mali da aka girke a wurin shakatawa na Kangaba, da ke wajen birnin Bamako, bayan harin da kungiyoyi masu da'awar jihadi suka kai wurin.. HABIBOU KOUYATE / AFP
Talla

Tun a watan Maris kasashe 5 na yankin Sahel, da suka hada da Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da Nijar, suka cimma jituwa kan kafa rundunar, a wani taro da suka yi a birnin Bamako, to sai dai ana bukatar amincewar MDD kafin ta fara aiki.

Wani lokaci a yau ake sa ran kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai kada kuri’ar amincewa da fara aikin rundunar.

A farkon watan da muke ciki, kungiyar tarayyar turai EU ta amince ta bayar da tallafin Euro miliyan 50 ga kasashen yankin Sahel din na G5 domin tafiyar da ayyukan rundunar, bayan da suka bukaci tallafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.