Isa ga babban shafi
Mali

Kungiyoyin da'awar jihadi sun dauki alhakin harin Mali

Kawancen kungiyoyin da ke ikirarin yin jihadi a yankin Magreb da Sahel, ya ce shi ne ke da alhakin kai harin shekaran jiya Lahadi, a wajen birnin Bamako na kasar Mali, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Motocin Sulke na majalisar Dinkin Duniya, da kuma na daukar marasa lafiya a wurin shakatawa da ke Kangaba, a kusa da birnin Bamako, Mali, a ranar Lahadin data gabata
Motocin Sulke na majalisar Dinkin Duniya, da kuma na daukar marasa lafiya a wurin shakatawa da ke Kangaba, a kusa da birnin Bamako, Mali, a ranar Lahadin data gabata AP Photo/Baba Ahmed
Talla

Sanarwar da wani shafin yada labarai da ke kasar Mauritania ya wallafa, ta jiyo kungiyoyin karkashinNusrat al-Islam wal Muslimeen, wadanda ake kallo a matsayin reshen Alqa’ida na cewa su suka tsara harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar, wato fararen hula 3 da kuma jami’an tsaro biyu da kuma wani adadi na maharan mai yawa.

Shaidun gani da ido sun ce, jami’an kungiyar tarayyar turai EU da na majalisar dinkin duniya, sun bukaci da a gaggauta turo Karin dakaru Mali da kuma sojin Faransa, a lokacin da aka fara musayar wuta da mayakan da ke da’awar jihadi a Kangaba.

A shekarar 2012, arewacin Mali ya koma karkashin ikon mayakan da ke da alaka da kungiyar Al-Qaeda, kafin daga bisani dakarun kasar Faransa, su sake kwato yankin arewacin kasar a watan Janairun shekarar 2013.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.