Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta ceto ‘yan ci-rani kusan 100 da suka makale a hamada

An ceto mutane 92 a cikin yankin hamada da suka kunshi mata da yara kanana a arewacin Jamhuriyar Nijar, bayan da wadanda ke jigilarsu suka yi watsi da su a kusa da Dirkou.

Italiya da Jamus sun bukaci Tarayyar Turai ta fadada tsaro a kan iyakokin Nijar da Libya domin dakile fataucin mutane zuwa Turai
Italiya da Jamus sun bukaci Tarayyar Turai ta fadada tsaro a kan iyakokin Nijar da Libya domin dakile fataucin mutane zuwa Turai AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Shugaban ofishin Hukumar Kula da Bakin Haure na MDD a birnin Yamai Giusepe Loperte, ya ce an yi watsi da wadannan mutane ne bayan da suka gaza biyan karin kudade ga wadanda za su tsallakar da su zuwa Libya.

Rahotanni sun ce an ceto mutanen kusan 100 a kusa da Achegour hanyar zuwa Libya.

A farkon watan Juni an tsinci gawarwakin wasu ‘yan ci-rani 44 da suka hada da yara da jarirai a yankin Agadez kan hanyarsu ta tsallakawa zuwa Turai.

A watan Mayu jami’an tsaron Nijar sun taba ceto wasu ‘yan ci-ranin na Afrika a hamada bayan masu fataucinsu sun yi watsi da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.