Isa ga babban shafi
Nijar

Yara na bukatar karatu a Diffa-UNICEF

Hukumar UNICEF da ke kula da ilimin yara kanana ta sake jaddada muhimmancin tura yara zuwa makaranta a Yankin Diffa Jamhuriyar Nijar, da ya yi fama da hare haren kungiyar Book Haram kusan shekaru biyu.

UNICEF ta ce Yara na son komawa Makaranta a Diffa.
UNICEF ta ce Yara na son komawa Makaranta a Diffa. UNHCR/K.Mahoney
Talla

Daraktar shiyar da ke kula da kasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka Marie-pierre Poirier ta bayyana haka a ziyarar da ta kai Diffa, inda ta bayyana muhimmancin tura yaran zuwa makaranta.

Alkalumma sun nuna cewar makarantu 166 aka rufe Nijar, kafin gwamnatin kasar da Hukumar UNICEF su sake bude makarantu 99 bara.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka makarantu kusan 30 ke rufe a Diffa da kusa da Kogin Komadougou da ke iyaka da Jihar Yobe.

Yara da Malamai na kauracewa Makarantu saboda barazanar hare haren ‘Yan Boko Haram. Amma babbar Jami’ar UNICEF Marie-Pierre ta ce a ziyarar da ta kai a yankin yara da dama sun nuna sha’awar komawa karatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.