Isa ga babban shafi
Sudan-Masar

Sudan da Masar sun gaza kawo karshen tsamin dangantaka

Wakilan kasashen Sudan da na Masar sun gaza cimma kyakkyawar matsaya a tattaunawar da suka yi jiya a birnin Alqahira, a kokarin kawo karshen tsamin dagantaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yayin da ya ke gabatar da jawabi a arewacin lardin Darfur mai fama da rikici, a ranar 7 ga watan Satumban shekara ta 2016, inda ya ke sanar da kawo karshen rikicin yankin Darfur a waccan lokaci.
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yayin da ya ke gabatar da jawabi a arewacin lardin Darfur mai fama da rikici, a ranar 7 ga watan Satumban shekara ta 2016, inda ya ke sanar da kawo karshen rikicin yankin Darfur a waccan lokaci. Ashraf Shazly/AFP Photo
Talla

Rikicin ya samo asali ne akan jayayyar mallakar yankin Halayeb, da ke kan iyakar kasashen biyu, wanda a yanzu haka ke karkashin ikon Masar, da Sudan ke da’awar nata ne.

Bayan kammala taron, ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Ghandour da takwaransa na Masar Sameh Shoukry, suka sanar da gaza cimma samun cigaba a zaman da suka yi.

A makon da ya gabata ne dangantaka ta kara yin tsami tsakanin kasashen biyu, bayan Sudan ta haramta shigo da kayan amfanin gona da ma dabbobi daga kasar Masar, bisa hujjar rashin inganci, zargin da gwamnatin Masar ta musanta.

Zalika a kwanakin baya Omar al-Bashir ya zargi Masar da bai wa ‘yan tawayen da ke fafatawa da sojinsa a yankin Darfur makamai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.