Isa ga babban shafi
Masar

Masar ta takaita aikin kungiyoyin fararen hula

Shugaban Masar Abdel Fatah al-Sisi ya rattaba hannu kan dokar kula da ayyukan kungiyoyin fararen hula, makatin da ‘yan rajin kare hakkin dan adam ke kallo a matsayin sabon yunkurin ci gaba da murkushe ‘yancin jama’a.

Shugaban Masar, Abdel Fatah al-Sisi
Shugaban Masar, Abdel Fatah al-Sisi KHALED DESOUKI / AFP
Talla

Kungiyoyin kare hakkin bil ‘adama sun ce, wannan doka da ta fara aiki ta haramta mu su gudanar da ayyukansu, abin da zai kawo nakasu ga kokarinsu na bai wa jama’a tallafin abinci da tufafi da magunguna har ma da ilimi.

Sabon matakin ya takaita ayyukan kungiyoyin a Masar tare da ayyana hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari ga duk wanda ya karya dokar .

Kazalika dokar ta bai wa kungiyoyin na fararen hula shekara guda da su amince da sabon matakin ko kuma kotu ta soke su baki daya a kasar.

A cikin watan Nuwamban bara ne dai, Majalisar Dokokin Masar ta rattaba hannu kan dokar wadda ke bukatar amincewar shugaba Abdul Fatah al-Sisi.

‘Yan rajin kare hakkin dan Adam sun ce, suna fuskantar cin zarafi mafi muni a tarihin kasar kuma a karkashin mulkin al-Sisi, in da suka zarge shi da shafe 'yancin walwalar da aka farfado da ita a shekarar 2011, a lokacin zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin shekaru 30 ta Hosni Mubarak.

Sai dai gwamnatin Masar ta ce dole ne ta dauki wannan matakin don kare kasar daga barazaanr tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.