Isa ga babban shafi
Najeriya

Osinbajo ya fadi nasarori da kalubalen gwamnatin Buhari

Yau Litinin ta kasance ranar dimokuradiyya a Najeriya, ranar da a bana ta zo daidai lokacin da shugaban da ke kan karagar mulkin kasar Muhammadu Buhari ya cika shekaru biyu da rantsuwar kama aiki.

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo
Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo REUTERS
Talla

Ana dai gudanar da bikin ne a daidai lokacin da shugaban ke jinya sakamakon rashin lafiyar da ya ke fama da ita, inda mukaddashinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya gabatar wa ‘yan kasar jawabi a madadinsa.

Jawabin mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa guda uku da suka hada da tsaro da yaki da rashawa da tattalin arziki.

Osinbajo ya ce ko shakka babu gwamnatinsu ta yi nasara sosai ta fannin tsaro musamman yakin da ake yi akan kungiyar Boko Haram, domin a yau ba wani yanki da ke karkashin ikon kungiyar, sannan gwamnatinsu ta yi nasarar ceto wasu daga cikin ‘yan Matan Chibok wadanda sace su ya tayar da hankalin duniya.

Osinbajo ya bayyana cewa an samu nasarar samar da tsaro a yankin Neja Delta mai arzikin mai, kamar yadda aka samu irin wannan nasara a fagen yaki da rashawa sakamakon samun goyo daga al’umma da ke tsegunta wa hukuma wadanda ke yi wa tattalin arziki zagon kasa.

Mukaddashin shugaban kasar na Najeriya ya danganta matsalar tattalin arziki a matsayin babban kalubalen da gwamnatin Buhari ta fuskanta.

“Tun lokacin da muka karbi mulki gwamnatinmu ta mayar da hankali ga matsalolin tattalin arzikin musamman tasirinsa ga wahalhalun da ‘yan Najeriya suke ciki”, a cewar Mukaddashin shugaban.

Osinbajo ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da yi wa shugaba Muhammadu Buhari addu’o’I domin samun sauki dangane da rashin lafiyar da ya ke fama ita a halin yanzu.

Sannan ya yi kira ga samar da hadin kai a tsakanin ‘yan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.