Isa ga babban shafi
Tanzania

Masu gadin dakin ajiyan gawa sun fasa cikin gawa sun sace miyagun kwayoyi

A kasar Tanzania ‘yan sanda na  tsare da wasu ma'aikata biyu na dakin ajiyan gawa dake Asibitin Dar es Salaam, wadanda  suka amsa cewa su suka fasa cikin wata gawa da aka kai ajiya suka sace tarin miyagun kwayoyi a cikin.

Shugaban 'yan sandan kasar Tanzania Said Mwema
Shugaban 'yan sandan kasar Tanzania Said Mwema RFI
Talla

Ma'aikatan biyu sun amsa cewa gawan wani mutun ne da aka kai asibitin da ake ganin ya mutu ne saboda ya sha miyagun kwayoyi da suka fi karfinsa.

Mutumin, a cewar ‘yan sanda dan kasar Ghana ne kuma an ganshi ne mace cikin dakin sa a wani Otel dake  Dar es Salaam, kuma aka kwashi gawan aka kai dakin ajiyan gawa na asibitin Mwananyamala, inda su ma'aikatan biyu suka fasa cikin gawan suka sace sunki-sunki 32 na miyagun kwayoyin dake cikinsa.

A cewar ‘yan sanda har mutanen biyu sun kai miyagun kwayoyin don saidawa

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.