EU zata karawa Jami’an Congo takukumai
Kungiyar Kasashen Turai ta ce tana nazarin karawa manyan jami’an Gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo Karin takunkumi saboda ci gaba da tashin hankalin da ake samu a kasar.
Wallafawa ranar:
Wata majiyar diflomasiyar kungiyar ta ce mutane tara takunkumin zai shafa wajen rufe asusun ajiyar su na bankuna da hana tafiye tafiye, saboda yadda suke taimakawa rikicin.
Kafin wadannan akwai wasu 7 da aka sanyawa takunkumin a watan Disambar bara, cikin su harda hafsoshin soji da 'Yan Sanda.
Zaman lafiya ya gaggara samuwa a Congo tun lokacin da Shugaba Joseph Kabila ya bayyana bukatar tsawaita wa'adin mulkinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu