Isa ga babban shafi
Congo

Shugaban ‘Yan tawaye ya tsere gidan yarin Congo

‘Yan tawayen Jamhuriyyar Congo sun fasa babban gidan yarin Kinshasa a yau Laraba inda suka yi awon gaba da shugabansu da ake tsare da shi da kuma wasu mabiya sama da 50.

Gidan yarin Goma a Jamhuriyyar Congo
Gidan yarin Goma a Jamhuriyyar Congo AFP PHOTO/Tony KARUMBA
Talla

Masu adawa da gwamnatin shugaba Joseph Kabila ne suka fasa gidan yarin wadanda suka rikide suka koma ‘yan tawaye.

Sun abka gidan yarin ne na Makala da sanyin asuba inda suka yi awon gaba da shugabansu Ne Muanda Nsemi da mabiyansa sama da 50.

Rahotanni sun ce da misalin karfe 4 na dare ne suka abka gidan yarin, kuma ‘yan tawayen sun samu taimakon mazauna yankin.

‘Yan tawayen sun yi bata-kashi da masu tsaron gidan yarin, kuma rahotanni na cewa da dama ne suka mutu. Kodayake zuwa yanzu babu cikakken bayani akan adadin fursunoni da jami’an gidan yarin da suka mutu.

Nsemi dai shi ke jagorantar kungiyar BDK a kudu maso gabashin Congo wadanda ke fafutikar neman ‘yancin yammacin kasar.

Fasa gidan yarin kuma na zuwa a daidai lokacin al’ummar Congo ke hutu domin cika shekaru 20 da hambarar da gwamnatin Mabuto Sese Seku wanda ya shugabanci kasar shekaru sama da 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.