Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Boko Haram 4 Najeriya ta bayar a madadin ‘Yan matan Chibok 82

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewar sun karbi fansar ‘Yan matan Makarantar Sakandaren Chibok 82 ne daga hannun Boko Haram bayan sun bada kwamandojin kungiyar hudu da gwamnati ta kama.

An yi musayar 'Yan Boko Haram 4 a kusa da Kumshe
An yi musayar 'Yan Boko Haram 4 a kusa da Kumshe REUTERS/Zanah Mustapha
Talla

Ministan Ma'aikatar harkokin Matan Kasar Hajiya Aisha Jummai Alhassan ce ta tabbatarwa RFI da adadin mayakn na Boko Haram ta gwamnati ta saki a madadin ‘Yan na Chibok.

Kuma ministan ta ce ko gobe suka sake samun irin wannan dama za su sake sakin wasu mayakan domin ceto sauran ‘Yan matan na Chibok da har yanzu suke hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

A ranar Asabar 6 ga Mayu aka saki 'Yan matan 82 bayan musayarsu da ‘yan Boko Haram a kusa da kumshe a Jihar Borno.

Boko Haram ta saki 'Yan Matan Chibok 82.
Boko Haram ta saki 'Yan Matan Chibok 82. REUTERS/Zanah Mustapha

Fadar shugaban kasa ta fadi cewa an shafe watanni ana tattaunawa da ‘Yan Boko Haram tare da shiga tsakanin kungiyoyin agaji da gwamnatin Switzerland inda kungiyar ta saki ‘Yan matan 82 a madadin wasu mayakanta.

A ranar 14 ga Afrilu ‘yan Boko Haram suka sace ‘yan matan 276 a makarantar Sakandaren mata ta Chibok a jihar Borno.

A watan Oktoban bara an kubutar da 21 daga cikinsu bayan wasu sama da 50 sun samu kubuta daga hannun 'Yan ta'addar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.