Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu ya tsallake rijiya da baya

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Taban Gai, inda suka raunata uku daga cikin masu tsaron lafiyarsa.

Wasu daga cikin mayakan 'yan tawaye masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu, Riek Machar a birnin Juba.
Wasu daga cikin mayakan 'yan tawaye masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu, Riek Machar a birnin Juba. Photo: Carl De Souza/AFP
Talla

To sai dai Ministan yada labaran sudan ta kudu Jacob Deng yace, mataimakin shugaban baya cikin ayarin a lokacin da aka bude musu wuta, kasancewar ya bi jirgin sama.

Ayarin dai na kan hanyarsa ce ta zuwa garin BOr daga babban birnin kasar Juba.

A shekara ta 2016 ce mataimakin shugaban kasa Taban Gai, ya shiga gwamnatin Salva Kiir, bayan ballewar da yayi daga bangaren ‘yan tawaye karkashin jagorancin Riek Machar.

Zargin yunkurin juyin mulki da shugaba Salva Kiir dan kabilar Dinka ya yiwa mataimakinsa Machar na kabilar Nuer, da kuma korarsa, ya haifar da kazamin fada tsakanin masu biyayya ga bangarorin guda biyu, wanda a yanzu ya juye zuwa fadan kabilanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.