Isa ga babban shafi
Somalia

Somalia ta kashe kwamandan al Shebaab

Gwamnatin Kasar Somalia ta ce ta kashe daya daga cikin shugabanin kungiyar Al Shebaab Moalim Osman Abdi Badil tare da wasu jami’ansa guda 3 a Yankin Shabelle. Wannan na zuwa bayan kisan wani Sojan Amurka.

al Shebaab na ci gaba da kai hare hare a Somalia
al Shebaab na ci gaba da kai hare hare a Somalia REUTERS/Ismail Taxta
Talla

Ministan yada labaran kasar ya ce sojojin Somalia ne suka kai harin da ya hallaka shugaban, kuma wannan ba karamar nasara ba ce a ci gaba da yakin da suke da Yan ta’adda.

A ranar juma’ar da ta gabata, kungiyar Al Shebaab ta kashe wani sojan Amurka guda tare da raunana wasu biyu.

Kasar Somalia ta kasa samun zaman lafiya tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Siad Barre a shekarar 1991.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.