Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya sake tafiya London

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi London daren jiya don sake ganawa da likitocinsa kamar yadda ya yi alkawari lokacin da ya koma gida watanni biyu da suka gabata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osibanjo a Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osibanjo a Abuja REUTERS
Talla

Mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fadi cikin wata sanarwa cewa Buhari ya rubuta wasika ga shugabannin Majalisun kasar domin sanar da su tafiyarsa London.

Shugaban ya shaidawa al’ummar Najeriya cewar babu wani abin fargaba dangane da halin da ya ke ciki.

Sanarwar tace likitocin da za su duba shi ne kawai za su iya bayyana kwanakin da zai yi.

Yanzu mataimakinsa Yemi Osibanjo zai ci gaba da tafiyar da harakokin gwamnati da ayyukan mulki kamar yadda aka saba.

Wannan ne ya kara dada haifar da cece-kuce a Najeriya kan rashin lafiyar shugaban, duk da ya fito sallar Juma’a bayan kauracewa taron ministocinsa sau uku.

Fadar shugaban dai za ta ci gaba da fuskantar matsin lamba kan fitowa ta bayyana asalin ciwon da ke damun Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.