Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya gana da ‘Yan matan Chibok 82

‘Yan matan makarantar garin Chibok 82 daga cikin sama da 200 da aka sace a Jihar Borno a 2014 sun gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa a Abuja bayan an yi musayarsu da mayakan Boko Haram da ake tsare da su.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da 'Yan Matan Chibok 82 da aka yi musaya da fursunonin Boko Haram
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da 'Yan Matan Chibok 82 da aka yi musaya da fursunonin Boko Haram twitter
Talla

Fadar shugaban kasa ta fadi cewa an shafe watanni ana tattaunawa da ‘Yan Boko Haram tare da shiga tsakanin kungiyoyin agaji da gwamnatin Switzerland inda kungiyar ta saki ‘Yan matan 82 a madadin wasu mayakanta da gwamnati ta saki.

An yi musaya da 'Yan matan 82 da ‘yan Boko Haram a garin Banki da ke kan iyaka da kasar Kamaru.

Sai dai gwamnatin Najeriya ba ta fadi adadin mayakan Boko Haram da ta saki ba domin ‘yan matan.

A ranar 14 ga Afrilu ‘yan Boko Haram suka sace ‘yan matan 276 a makarantar Sakandaren mata ta Chibok a lokacin da suke shirin rubuta Jarabawa. A watan Oktoban bara an kubutar da 21 daga cikinsu bayan wasu sama da 50 sun samu kubuta daga hannun 'Yan ta'addar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.