Isa ga babban shafi
Nijar

Masu dakon kaya na yajin aiki a Nijar

Yanzu haka daruruwan motoci ne dauke da kaya suka fara yajin aiki a sassa daban daban na Jamhuriyar Nijar, inda suke nuna adawa da wani sabon tsarin biyan kudin sikeli da aka fara amfani da shi a jiya litinin a kasar.

Masu dakon kaya na yajin aiki a Nijar
Masu dakon kaya na yajin aiki a Nijar RFIHAUSA/Awwal
Talla

Masu motocin dakon kayan sun bayyana wannan mataki a matsayin wanda ya saba wa dokokin kasashen yankin yammacin Afrika da ke amfani da takarar da kudin cfa wato UEMOA.

Hima Barkire daya daga cikin shugbannin kungiyar masu motocin dakon kayan ya shaidawa RFI Hausa cewa hukumomin Nijar sun tsawwala dokokin inda ake masu awo daga Kwanni da Dosso har zuwa Yamai.

Masu dakon sai sun biya kudi bayan auna kayansu kafin su wuce. Barkire ya ce ya dace gwamnati ta yi shawara da su kafin aiwatar da matakin.

Kungiyar UEMOA ta kunshi Benin da Burkina Faso da Mali da Nijar da Senegal da Togo da Cote d’Ivoire da kuma Guinea Bissau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.