Isa ga babban shafi
Mali

Sojojin Faransa sun kashe 'yan bindiga 20 a Mali

Sojojin Faransa da ke fada da ayyukan ta’addanci a Mali, sun sanar da kashe ‘yan bindiga sama da 20 a yankin da ke kusa da iyakar Mali da Burkina Faso.

Sojojin da ke aikin wanza da zaman lafiya a Mali
Sojojin da ke aikin wanza da zaman lafiya a Mali AFP/Thomas Coex
Talla

Dakarun na Faransa sun kaddamar da farmaki ne da nufin kakkabe ‘yan ta’adda a wani gandun daji da ake kira Foulsare kusa da iyakokin kasashen biyu, kuma mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Faransa Kanar Patrick Steiger, an kashe ‘yan ta’adda fiye da 20.

Gwamnatin Mali dai ta tsawaita yin aiki da dokar ta baci da watanni shida a nan gaba, domin ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda a kasar.

Gwamnati ta ce an tsawaita aiki da dokar ne domin karfafa wa jami’an tsaro gwiwa, tare da kara ma su karfin iko lura da yadda har yanzu ake ci gaba da samun hare-hare daga ‘yan ta’adda a sassa da dama na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.