Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Shari'ar jami'an tsohuwar gwamnatin Burkina Faso

Babbar Kotun Shari’a a Burkina Faso za ta fara shari’ar tsoffin jami’an gwamnatin kasar a karkashin jagorancin tubabben shugaban Blaise Compaore, wadanda ake zargi da kashewa da kuma azabtar da masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatinsu.

Tsohon shugaban Burkina Faso a tsakiyar ministocinsa a shekara ta 2013
Tsohon shugaban Burkina Faso a tsakiyar ministocinsa a shekara ta 2013 AHMED OUOBA / AFP
Talla

Tsohon Firaminista Luc Adolphe Tiao da ministocinsa, za su gurfana a gaban kotun, yayin da tsohon shugaba Compaore ke gudun hijira a makociyar kasar Cote d’Ivoire.

A tarzomar da ta barke cikin watan okotban 2014, jami’an tsaro sun yi amfani da karfi akan jama’a har aka samu asarar rayukan mutane da dama, yayin da wasu suka samu raunuka.

Bayanai na nuni da cewa za a dauki akalla mako daya ana wannan shara’a, irinta ta farko a tarihin kasar da ke yankin yammacin Afirka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.