Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kashe Sojojin Kamaru uku

Akalla Sojojin Kamaru uku ne suka mutu a sannan kimanin biyar suka jikkata bayan sun taka nakiya da kungiyar Boko Haram ta dasa a yankin arewacin kasar. Wannan na a yayin da a Najeriya rahotanni suka ce Boko Haram ta kashe mutane hudu a harin kunar bakin wake da ta kai a garin Maiduguri a yau Litinin.

Sojojin Kamaru da ke fada da Boko Haram na Najeriya
Sojojin Kamaru da ke fada da Boko Haram na Najeriya AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Sojojin sun taka nakiyar ne a garin Mora a cikin motar da ke dauke da su, kamar yadda wata majiyar Sojin Kamaru ta tabbatar.

Kuma majiyar ta ce kimanin sojoji uku suka mutu nan take, biyar suka jikkata.

Kamaru dai na cikin rundunar sojin kasashen tafkin Chadi da ke fada da Boko Haram.

Boko Haram kuma ta kashe Sojojin kasar da dama ta hanyar dasa nakiya a yankin arewa mai nisa.

Wannan na zuwa a yayin da wasu rahotanni daga Najeriya ke cewa mutane hudu sun mutu a Maiduguri a harin kunar bakin wake da Boko Haram ta kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.