Isa ga babban shafi
Nijar

An soma biyan kudaden alawus na Dalibai a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, kungiyar dalibai ta kasa USN  ta sanar da cimma jituwa da Gwamnatin Mahamadu Issifou.An dai share kusan mako daya ana tattaunawa tsakanin wakilan daliban da gwamnatin kasar ta Nijar, wacce ta yi naam da wasu daga cikin bukatun daliban. 

Dalibai masu zanga -zanga
Dalibai masu zanga -zanga
Talla

Bukatun dai sun hada da sako daliban da yan Sanda suka kama, biyan daliban kudaden alawus tareda sake bude jami’ar Abdoul Moumouni Diffo dake babban birnin Yameh.

Shugaban kasar a cewar majiya daga fadar sa ya umurci hukumar ANAB wacce ke da nauyi biyan dalibai kudaden alawus soma biyan daliban wanda tuni aka soma daga Yameh zuwa wasu biranen kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.