Tsutsar da ke yin ta’adi a gonakki ta bulla a Rwanda da Kenya
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka tsutsar nan da ke cinye amfanin gona ta isa kasashen Rwanda da Kenya, bayan ta’adin da ta yi a wasu kasashen da ke kudancin Afirka.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Uganda ta tabbatar da isar tsutsar gonakin kasar, inda ta zama kasa ta uku a Gabashin Afirka da ke fuskantar matsalar.
Telesphore Ndabamenye, shugaban hukumar samar da iri a Rwanda, yace tsutsar ta mamaye gonaki a Yankuna 30.
Jaridar Kenya ta ruwaito cewar tsutsar ta bulla a Yankuna 11 daga cikin Yankuna 47 da ke kasar.
Tsutar dai na yin barazana ga manoma, da suke fuskantar matsalar fari.
Tsutsar ta fi yin illa ga hatsi kamar Masara da alkama da gero da shinkafa.
Yawancin mutanen kasashen Afrika dai na dogaro ne da arzikin noma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu