Isa ga babban shafi
Congo

An Sake gano kaburbura a Congo

Masu Bincike na Majalisar dinkin Duniya sun ce sun gano manyan kaburbura 17 a tsakiyar Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, abinda ya kawo adadin kaburburan da aka samu zuwa 40.

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Congo
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Congo Photo MONUSCO/Force.
Talla

Ana zargin sojojin gwamnati da kashe fararen hula 74 cikinsu har da yara kanana 30 a tashin hankalin da aka samu a Yankin kasai tsakanin su da Yan kabilar Kamuina Nsapu.

Ya zuwa yanzu gwamnatin Congo ba ta ce komai kan wannan bincike ba.

A watan Agustan bara ne rikici ya barke a Kasai, bayan jami’an tsaron Congo sun kashe shugaban kabilan yankin, Jean Pierre Mpandi, saboda ya jagoranci gangamin adawa da shugaba Joseph Kabila.

Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra’ad Al Hussein, ya fadi a cikin wata sanarwa cewa jimillar kaburbura 40 yanzu aka gano a yankin Kasai bayan gano wasu 17 a Tshimbulu da kauyen Tshienke.

Mista Zeid ya ce, sake gano kaburburan ya kara tabbatar da mumunan ta’asar da aka tabka a yankin a cikin watanni 9 da suka gabata.

Zeid ya kuma ce ya zama dole, gwamnatin demukuradiyar congo ta kaddamar da bincike tare da daukar matakan tsaro, na kaucewa kisa da keta hakkin bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.