Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana boye kudade hatta ma a cikin makabartu a Najeriya

Ministan watsa labarai da al’adu na tarayyar Najeriya Lai Mohamed, ya ce tabbas shirin yaki da rashawa na gwmanatinsu na samun hadin-kai daga jama’ar kasar, kuma wannan ne dalilin samun nasarar shirin.

Tambarin Hukumar Yaki da Rashawa a Najeriya
Tambarin Hukumar Yaki da Rashawa a Najeriya RFI / Pierre Moussart
Talla

Ministan wanda ke zantawa da manema labarai a birnin Lagos, ya ce duk da cewa akwai tukuici na musamman da aka ware domin bai wa wadanda ke taimaka wa hukumar yaki da rashawa ta kasar EFCC da bayanai don gano wadanda ke boye dukiyar kasar, to amma da dama daga cikin masu bayar da bayanan na yin haka ne saboda kishin kasa amma ba domin kudi ba.

Lai Mohamed ya ce sau da dama suna samun bayanai daga jama’a da ke tabbatar da cewa mafi yawa daga cikin kudaden da aka sace, ana turbude su ne a cikin gidaje ko a cikin kungurmin dawa, yayin da wasu ke boye kudaden a makabartu.

To amma duk da haka hukumar ta yaki da rashawa na samun nasarar kwato dukiyar gwamnati a cewarsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.