Isa ga babban shafi
Faransa-Africa

Shugaba Hollande ya baiwa wani gungun tsofin sojan mulkin mallakar kasar, takardun zama Faransawa

Shugaba François Hollande na Faransa, ya lamunce wa wani gungun tsofin sojan mulkin mallaka su 28, daga kasashe da dama na Afrika damar zama faransawa. Ana sauran ‘yan makwanni wa’adin mulkinsa ya kawo karshe ne, shugaba François Hollande, ya bukaci girmama wadannan sojoji na mulkin mallaka da suka yi yake yake da sunan faransa har zuwa lokacin samun ‘yancin kai a shekarun 1960.  

tirailleurs senegalais
tirailleurs senegalais GEOFFROY VAN DER HASSELT / AFP
Talla

An gudanar da shagulgulan ne tare da nuna hoton bidiyon tsofin sojin (‘yan asalin kasashen Senegal, Congo, Afrika ta Tsakkiya da kuma kasar Cote d’Ivoire da suka yi yaki da sunan Faransa a yakin Indochine da na kasar Aljeria

An samar da rundunar dakarun mulkin mallakar taya Faransa yaki ta ‘kasar Senegal ne a shekarar 1857, karkashin gwamnan mulkin mallaka Louis Faidherbe.

Hoton bidiyon na tarihi marar kala da aka haska, ya nuna wadannan sojoji na mulkin mallaka na barin wuta a fagen daga.

A lokacin da yake tofa albarkacin baki, a wata fira da aka yi dashi bada jimawa ba, wani tsohon dakaren mulkin mallakar M. Ndongo mai shekaru 82 a duniya, cewa , ya yi yaki domin Faransa a Aljeria, don a kasance sauke nauyi ne, kuma abin alfahari.

Dottijon ya nanata bukatar son komawa kasarsa ta farko Faransa.

A cikin jawabin da ya gabatar shugaban jamhuriya Francois Hollande ya tunatar da cewa, baiwa wadannan tsofin sojoji takardar zama faransawa, wadanda a yau ke da manyan shekaru, ba komai yake nufi ba face gyara ga rashin adalcin da aka tafka a baya, kai ta ma kai shugaba François Hollande ga maganar « bashin jini » da yace Faransa ta karba daga wadannan sojoji da suka taya ta yaki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.