Isa ga babban shafi
Somalia-Amruka

A karo na farko cikin shekaru 23 Amruka ta tura da sojoji a kasar Somaliya

A karo na farko tun cikin 1994, Amurka ta aika da dakaru soja a Somaliya domin taimakawa sojan kasar a yakin da suke da mayakan kungiyar al Shebab.Tura wadannan sojoji dai na zuwa ne sakamakon bukatar hakan da gwamnatin Somaliya ta gabatarwa Amruka.  

sojojin kenya a kasar Somaliya
sojojin kenya a kasar Somaliya © STRINGER / AFP
Talla

Daga wakilinmu a Washington, Jean-Louis Pourtet

Sama da dakarun Amruka 40 na rundunar ta 101 ta sojan saman Amruka ne, yanzu haka suka isa a Mogadiscio, karkashin gudummawar Amruka ta karfafa rundunar sojan Somalia a yakin da ta ke yi da mayakan shebab.

A wani sakon wasika da ya aikawa tashar Tv ta CNN, kakakin rundunar sojan Amruka a nahiyar Afrika (Africom), Charles Chuck Prichard, ya ce an tura sojojin ne a karakashin bukatar da mahukumtan somaliya suka gabatar ga Amruka ne.

Aikin da ya rataa a wuyan wannan tawaga ta Amruka dai shi ne, bada horo tare da taimakawa dakarun na Somalia da kuma na kungiyar tarayyar Afrika dake yaki da al Shebab a kasar ta Somaliya.

Aikin wadannan dakaru na Amruka dai ya sha bamban da wanda wasu mashawarta amerikawa ke gudanarwa yanzu haka a kasar ta Somaliya ne, wanda ya ta’alaka wajen bada shawarwari da dubarun yaki da ayukan ta’addanci, ba tare da halartar fagen daga ba.

Za a iya ewa dai rabon da sojan kasar Amruka su tsaya a cikin Soaliya tun bayan mutuwar dakarun kasar 18 a shekarar 1994 sakamakon kakkabo jirginsu mai saukar agulu da mayaka suka yi a birnin Mogadiscio.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.