Babu ribar da Nijar ta samu daga kamfanin Areva
Wasu kungiyoyi uku masu zaman kansu ONE, Oxfam da kuma Sherpa, sun ce ba wata ribar da gwamnatin Nijar ta sama a cinikin Uranium tsakaninta da kamfanin Areva a wani rahoton da suka fitar a jiya alhamis.
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin sun ce kudaden da Nijar ta karba ba su taka kara sun karya ba duk da cewa bangarorin biyu sun tattauna tare da sabunta yarjejeniyar da ke tsakaninsu ta wannan bangare.
Kungiyoyin sun kalubalanci kamfanin na Areva da kuma gwamnatin Nijar da su fito su bayyana wa duniya kudaden da ake samu a ciniki.
Rahoton ya ce a tsakanin shekara ta 2014 zuwa 2015, kudaden da Nijar ke samu daga Uranium sun ragu da kimanin Euro milyan 15 ba tare da wani dalili ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu