Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya sun tarwatsa matatun da ake satar mai a Neja Delta

Rundunar Sojin Najeriya ta ce jami’anta sun tarwatsa wasu matatun mai 13 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a yankin Neja Delta mai arzikin fetir a wani babban farmakin da ta kaddamar da ya yi sanadin salwantar rayukan sojoji guda biyu.

Sojojin Najeriya sun kaddamar da yaki da tsagerun yankin Niger Delta mai arzikin fetir
Sojojin Najeriya sun kaddamar da yaki da tsagerun yankin Niger Delta mai arzikin fetir (Photo : Reuters)
Talla

Kakakin rundunar sojin ta Najeriya Manjo Abubakar Abdullahi ya ce akwai daruruwan matatun mai da aka kafa suna aiki ba kan doka ba wadanda ake amfani da su wajen tace man da ake sacewa, kuma a jiya laraba sun tarwatsa 13 a Iyalama Adama cikin jihar Rivers.

Wannan dai ya yi karo da kudirin gwamnati a baya na kokarin halatta matatun man domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Babban kwamandan rundunar sojin ruwa ya bayyana cewa kimanin matatun mai 181 aka tarwatsa a bara sannan mutane 748 aka cafke wadanda ake zargi da satar danyen mai.

Jami’an tsaron sun ce sun kwato danyen mai da darajarsa ta kai Naira biliyan 420 daga matatun man da aka kafa ba kan ka’idar doka ba.

Najeriya dai na dogaro da arzikin fetir, amma matsalar satar mai da tsagerun Neja Delta da ke fasa bututun mai ya karya tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.