Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 4 sun mutu a rikici tsakanin Sojoji da ‘Yan sanda a Yobe

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar soja daya da kuma ‘yan sanda uku, sakamakon wani artabun da aka yi a jiya Laraba tsakanin bangarorin biyu a garin Damaturu na jihar Yobe da ya yi fama da rikicin Boko Haram.

Sojoji da 'Yan sanda na gudanar da aikin tsaro na hadin guiwa a arewa maso gabas da ke fama da rikicin Boko Haram a Najeriya
Sojoji da 'Yan sanda na gudanar da aikin tsaro na hadin guiwa a arewa maso gabas da ke fama da rikicin Boko Haram a Najeriya Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar Jimoh Moshood ya ce suna da masaniya a game da rikicin, inda ya ce za a bincike musabbabin faruwarsa.

Bayanai na cewa rikicin ya samo asali ne a lokacin da motar wani jami’in soji a cikin farin kaya ta gogi daya daga cikin motocin ‘yan sanda, wanda suka yi masa duka, kuma daga nan ne aka ce sauran sojoji sun afka wa ‘yan sandan domin daukar fansa.

Rahotanni sun ce harbin bindiga ne ya haifar da hasarar rayuka a rikicin tsakanin Sojoji da ‘Yan sandan, yayin da wasu suka jikkata.

Yobe dai na cikin jihohin da ke fama da barazanar Boko Haram, inda Sojoji da ‘Yan sandan Najeriya ke gudanar da aiki tsaro na hadin guiwa tare da taimakon dakarun kasashen ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.