Amurka ta kakabawa wasu ‘Yan Seleka da Balaka takunkumi
Amurka ta sanya takunkumai a kan shugabannin wasu kungiyoyin ‘yan daba guda biyu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sakamakon rawar da suke takawa wajen tunzura jama’a da rikicin kasar mai nasaba da kabilanci da addini.
Wallafawa ranar:
Wadanda matakin ya shafa sun hada da Abdoulaye Hisseme tsohon shugaban Seleka, da kuma wani mai suna Maxime Mokom jigo na kungiyar Anti-Balaka.
Sannan takunkumin ya haramtawa Amurkawa da kamfanonin kasar yin hulda da mutanen inda aka kuma rufe asusun ajiyarsu a Amurka.
Rikicin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ya kashe daruruwan mutane tare da raba dubbai da gidajensu.
An zargi mutanen ne da kokarin yamutsa kuri’ar raba gardama kan kundin tsarin mulki da gudanar a 2015 tare da yin zagon kasa ga jagorancin shugaba Faustin-Archange.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu