Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar sun kashe Yan Boko Haram 57

Wata majiyar tsaro a Nijar ta ce sojojin kasar sun kashe mayakan Boko Haram akalla 57 a wata musayar wuta da suka yi a kusa da garin Gueskerou da ke cikin Jihar Diffa yankin kudu masu gabashi da ke kan iyaka da Najeriya.

Sojojin hadin guiwa na kasashen tafkin Chadi da ke yakar Boko Haram
Sojojin hadin guiwa na kasashen tafkin Chadi da ke yakar Boko Haram © Getty Images
Talla

Akwai babban kwamandan Boko Haram daga cikin mayakan da aka kashe, kamar yadda majiyar sojin ta tabbatarwa kamfanin dillacin labaran Faransa.

Sojojin Nijar sun yi nasarar fatattakar Yan Boko Haram ne bayan sun shigo garin cikin mota da Babura a ranar Lahadi.

Sannan Sojojin sun yi nasarar kwato tarin makamai daga hannun mayakan na Boko Haram.

Majiyar da ta tabbatar da labarin ta ce akwai sojoji da dama da suka samu rauni a musayar wutar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.