Patrice Talon ya fasa yi wa kundin tsarin mulki gyara
Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon ya ce ya dakatar da aniyarsa ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara bayan ya gagara samun hadin kai daga ‘yan majalisu.
Wallafawa ranar:
Shugaba Patrice Talon ya sanar da wannan mataki ne lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanaki biyu bayan da ‘yan majalisar kasar suka ki amincewa da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara wanda haka zai dawo da wa’adin shugabancin kasar shekaru 6 sau daya kacal.
Majalisar Jamhuriyar Benin dai ta ki amincewa da bukatar sauya kundin tsarin mulkin wanda zai rage wa’adi mulkin shugaban kasar, zuwa wa’adi guda daga wa’adi biyu da akeyi yanzu haka.
Yan Majalisu 60 suka amince da bukatar, amma kuma 22 suka ki, kuma kundin tsarin mulkin kasar yace dole sai an samu kasha 4 bisa 5 kafin dokar tayi nasara.
Shugaban kasa Patrice Tallon ya nemi yin chanjin na ganin an rage wa’adin mulkin shugaban kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu