Isa ga babban shafi
Somalia

Farmajo ya Kaddamar da sabon yaki kan al-Shabaab

Sabon shugaban kasar Somalia, Muhd Abdullahi Farmajo ya bayyana kaddamar da sabon yaki kan mayakan al-Shabaab.

Shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo
Shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo REUTERS/Feisal Omar
Talla

Shugaban ya kuma yi tayin afuwa ga duk mayakin al-Shabaab da ya mika makamansa cikin kwanaki 60, tare gargadin wadanda suka ki, su kuka da kansu.

Gargadi hade da tayin afuwan daga shugaban ya zo ne kwanaki biyu, bayan fashewar wani bam da aka dana jikin mota da ya hallaka mutane bakwai a wani gidan cin abinci da ke birnin Mogadishu.

Yayin shelar kaddamar da sabon yakin, Shugaba Farmajo ya kuma yi alkawarin bada kyautar Dalar Amurka dubu 100 ga duk wanda ya bada bayanan da za su taimaka wajen gano maboyar masu dasa bama-baman.

Kamfanin dillancin labaran faransa AFP ya rawaito cewa akalla mutane 80 ne hare haren bam  ya kashe a Mogadishu daga watan Janairun shekarar 2017 zuwa yanzu.

Tun bayan korar mayakan al-Shabaab da dakarun kungiyar kasashen Afrika suka yi a shekara ta 2011, mayakan al-Shabaab suka zafafa kai hare haren sari ka noke a babban birnin Somalia, Mogadishu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.