Hukuncin mika wasu tsibirai daga Masar zuwa Saudiya
Wata Kotu a kasar Masar ta yanke hukunci mikawa kasar Saudi Arabia wasu tsibirai guda biyu da ake takaddama a kai, wanda a baya ya haifar da zanga zanga.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An dai amince da shirin mikawa Saudiya wadannan tsibirai guda biyu ne a watan Afrilun bara, bayan Sarki Salman bin Abdulaziz ya ziyarci kasar, ya kuma mikawa kasar kyauta na kasaita, wanda mutane ke zargin cewar sayar da tsibiran aka yi.
Sakataren kwamitin harkokin waje na Majalisar dokoki Tarek Al Khouli ya ce gwamnati ta mikawa Majalisar bukatar mika tsibiran biyu, amma ya zuwa yanzu ba suyi mahawara a kai ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu