An zargi sojin Sudan ta Kudu da kone gidaje sama da 3,000
Kungiyoyi masu zaman kansu da ke sa’ido kan yakin da ake fafatawa a kasar Sudan ta Kudu, sun ce sojin gwamnati sun kone dubban gidajen fararen hula a karshen shekara ta 2016 da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Rahoton da masu fafutukar suka fitar, na daga cikin zargin cin zarafin dan ‘adam mafi karfi da ake kan sojin Sudan ta Kudu a cikin shekaru 3 da kasar ta shafe cikin yakin basasa.
Jami’an sa ido da suka kaiwa kauyuka 3 ziyara a yankin Yei da ke kudancin kasar, sun ce a kauye guda kadai, sojin kasar sun kone gidaje akalla dubu uku.
Sai dai gwamnatin kasar ta musanta zargin inda ta dora laifin kone gidajen da kuma sauran laifukan yaki na take hakkin dan'adam da ke aukuwa a kasar, kan mayakan ‘yan tawaye, sai kuma wutar daji da gwamnatin kasar ta ce ita ce silar konewar mafi yawancin gidajen fareren hular a kauyukan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu