Isa ga babban shafi
RFI

Gogaggen dan jaridar RFI Laurent Sadoux ya rasu

Rasuwar Laurent Sadoux gogaggen Dan jaridar RFI sashen Faransanci ya girgiza masu saurare musamman jimamin muryarsa da kuma kwarewarsa wajen gabatar da Labarai.

Marigayi Laurent Sadoux
Marigayi Laurent Sadoux ®Pierre René-Worms/RFI
Talla

Baya ga Masu sauraren RFI, Labarin rasuwar Sadoux ya ja hankalin mutane a shafukan sadarwa na Intanet musamman Facebook da Twitter.

Kimanin mutane dubu 4 suka wallafa hoton Sadoux a facebook yayin da labarin rasuwarsa da sashen Faransanci na RFI ya wallafa ya samu tsokacin mutane sama da dubu 5 inda suke bayyana jimamin rasuwarsa da kuma yadda za su yi kewar labaransa da ya ke gabatarwa cikin raha a sashen Faransanci musamman labaran Afrika.

Sadoux ya shafe shekaru 17 yana gabatar da labaran Afrika a sashen Faransanci tun a shekarar 2000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.