Isa ga babban shafi
Najeriya

Sankarau ya lakume rayuka 270 a Najeriya

Akalla mutane 270 akasari yara suka rasa rayukansu bayan kamuwa da ciwon sankarau a cikin watanni 5 a Najeriya.

Sankarau ya lakume rayuka 270 a Najeriya
Sankarau ya lakume rayuka 270 a Najeriya AFP
Talla

Cibiyar da ke kula da yaduwar cututtuka ta kasa ta ce yanzu haka akwai mutane 1,828 dauke da ciwon, kuma 269 sun mutu a jihohi 15 na kasar.

Sokoto da Zamfara da Katsina da Kebbi da Niger sai Abuja ne Ciwon yafi tsanani kuma ana ne aka samu asaran rayuka da dama

Daraktan sashin takaita yaduwar cututtuka a ma’aikatar lafiya ta kasa, Dr. Nasir Sani Gwarzo, ya ce a wadanan jihohin 6 aka samu mutane 1,090 da ke dauke da Sanakarau da mutuwar mutane 154.

Dr. Nasir ya ce a Zamfara kawai mutane 590 ne suka kamu da Ciwon kuma 29 sun mutu. Kana ya bayyana nau’in Ciwon da wanda ba a saba gani irinsa ba.

Hukumar lafiya ta WHO ta ce yara masu shekaru 5 zuwa 14 ne suka fi kamuwa da Ciwon kuma suke mutuwa.

Tuni aka soma rigakafin gaggawa a cewar Dr. Nasir Gwarzo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.