Sudan ta Kudu na siyan makamai a cikin yunwa
Wani rahoton sirri da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce, gwamnatin Sudan ta Kudu na amfani da kudaden da ta samu a harkar man fetir wajen siyan makamai, a dai dai lokacin da kasar ke fama da matsalar yunwa.
Wallafawa ranar:
Rahoton wanda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya samu , ya bukaci a dakatar da siyar wa Sudan ta Kudu da makamai, matakin da kasar Amurka ta amince da shi amma Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da shi a kuri’ar da ya kada a cikin watan Disamban da ya gabata.
Gwamnatin Sudan ta Kudu dai na ci gaba da sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayyar makamai duk da sanarwar da ke cewa, al’ummar kasar na mutuwa saaboda yunwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu