Isa ga babban shafi
Madagascar

Guguwar Cyclone Enawo ta kashe mutane 50 a Madagascar

Gugguwar Cyclone Enawo ta kashe mutane 50 tare da raba mutane dubu 176 da muhallinsu a Madagascar.

Guguwar Cyclone Enawo ta yi barna a Madagascar
Guguwar Cyclone Enawo ta yi barna a Madagascar
Talla

Hukumar agajin gaggawa kasar da ke tabbatar da alkalluman mamatan ta ce mutane dubu 53 ne kuma suka bata sakamakon guguwar da ta auku cikin wannan makon.

Hukumar ta ce yanzu haka akwai cibiyoyi sama da 130 da ke karban wadanda guguwar ta sha fa.

Hotuna bidiyo sun nuna yadda gugumar mai karfin gaske ta share gidaje da bishiyu da tittuna bayan haifar da ambaliya.

Ana kyautata zaton wadanda guguwar ta yi wa ta'adi su zarta dubu 700 la'akari da cewa shi ne irinsa mafi muni da kasar ke fuskanta tun bayan shekarar ta 2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.