Isa ga babban shafi
Senegal

Za a kare masu fallasa barayin gwamnati a Afrika

Masu rajin kare hakkin dan Adam a Afrika da wasu Lauyoyi, sun kaddamar da wani shirin kare masu fallasa barayin gwamnati a nahiyar. Shirin wanda aka kaddamar a kasar Senegal, zai bai wa masu fallasar damar gudanar da aikinsu cikin sauki.

Gwamnatin Buhari a Najeriya ta kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa.
Gwamnatin Buhari a Najeriya ta kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shirin zai bai wa masu fallasa barayin kudaden talakawa a nahiyar Afrika kariya ta fannin shari’a, sannan kuma zai kare su a aikinsu na bada bayanan da suka samu.

Masu ruwa da tsaki wajen samar da wannan shiri sun ce, za a samar da wata hanyar sadarwa ta musamman da ‘yan tonon sililin za su rika amfani da ita.

Wani kwararren lauyan Spain mai suna Mista Baltasar Garzon da takwararnsa na Faransa mai suna William Bourdon da kuma wani dan rajin kare hakkin dan Adam a Senegal Alioune Tine, su ne suka kirkiro shawa’ar samar da wannan shiri.

Kwararrun guda uku sun ce, dalilin shirin shi ne sanar da Jama’ar Afrika girman cin hanci da take hakkin dan Adam da shugabanninsu ke yi.

Kwararrun sun ce, sun yanke shawarar bai wa masu fallasa miyagun aikin kariya a Afrika, nahiyar da wannan aikin ke fuskantar babban hatsari, domin kuwa wani lokacin ana garkame masu fallasar a gidan yari ko kuma a kashe su har lahira.

Ana yawan zargin manyan jami’an gwamnatin Afrika da wawushe dukiyar talakawa don azurta kansu.

Kasashen Afrika ne sahun karshe a jerin kasashen da matsalar rashawa ta fi yin kamari, musamman Somalia da Sudan ta kudu da Libya da Guinea-Bissau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.