Isa ga babban shafi
Somalia

Mutane 110 suka mutu sakamakon yunwa cikin kwanaki biyu a Somalia

Firaministan kasar Somalia Hassan Ali Khaire ya sanar da cewa cikin kwanaki biyu da suka gabata 'yan kasar 110 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon yunwa da gudawa. 

Wani sabon gini a tsakiyar birnin  Mogadishu, Somalia
Wani sabon gini a tsakiyar birnin Mogadishu, Somalia CC/Wikimedia
Talla

Tun a watan jiya ne dai Hukumar kulada da yara kanana ta MDD ta sanar da cewa Somalia na cikin hatsarin gaske domin yara kananan da suka kai dubu 270 za su kamu da matsanancin laulayi na yunwa.

Firaministan ya ce mutan kasar da suka kunshi makiyaya da dabbobinsu na cikin hatsarin gaske sakamakon yunwa dake kara muni.

Ya ce Gwamnati za ta yi iyakacin kokarinta, amma kuma akwai bukatar ‘yan kasar dake koina su taimaka a fita daga matsanancin matsalar yunwan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.