'Yan adawa na zanga-zanga a Nijar
Gungun ‘yan adawa a Nijar sun fito suna zanga-zanga a yau a birnin Yamai ta kin jinin gwamnatin shugaba Mahamadou Issoufou tare da neman ganin an ba bangaren shari’a ‘yanci.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
‘Yan adawar kuma na kukan tsadar rayuwa da matsalar cin hanci da rashawa da rashin tafiyar da gwamnati ta hanyar da ta dace.
Masu zanga-zangar dai sun mamaye harabar majalisa a Yamai suna yayata cewa “Tayi Tauri, ka fice ya isa haka nan”.
Bukatun masu zanga-zangar kuma sun hada da neman a saki fursunonin siyasa da aka cafke a shekarar 2015 kan zargin yunkurin juyin mulki, sannan sun bukaci ficewar dakarun Faransa da Amurka da Jamus da suka kafa sansanonin yakar ‘yan ta’adda a Mali da Libya.
Zanga-zangar dai ta yi karo da wadda aka taba gudanarwa a watan Janairu da ke nuna goyon baya ga jagorancin shugaba Mahamadou Issoufou.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu