Isa ga babban shafi
Mali

Kungiyoyin ta’adda uku a Sahel sun hada kai

Manyan kungiyoyin ta’adda guda uku da ke barazana a yankin Sahel sun sanar da hadewa a matsayin kungiya guda da za ta kunshi dukkanin mayakansu. Kungiyoyin sun sanar da hadewa ne a cikin wani sakon bidiyo da suka aika wa Kamfanin dillacin labaran Mauritania ANI.

Shugaban Ansar Dine ta Mali Iyag Ag Ghalya tsakiya shi ne sabon shugaban kungiyoyin ta'adda da suka dunkule a yankin Sahel
Shugaban Ansar Dine ta Mali Iyag Ag Ghalya tsakiya shi ne sabon shugaban kungiyoyin ta'adda da suka dunkule a yankin Sahel ANI
Talla

Kungiyoyin uku sun kunshi kungiyoyin ta’ adda biyu a Mali Ansar Dine da ‘yan tawayen Macina Brigades da kuma kungiyar Al Murabitoun ta Algeria, dukkaninsu da ke da alaka da Al Qaeda.

Kungiyoyin sun amince da kafa sabon suna a matsayin kungiyar da ke taimako addinin Islama da musulmi karkashin jagorancin Iyag Ag Ghaly shigaban Ansar Dine ta Mali.

A cikin sakon bidiyon, shugaban kungiyoyin Ag Ghaly ya kara jaddada mubaya’arsu ga shugaban Al Qaeda Ayman al Zawahiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.