Isa ga babban shafi
Gambia

Adama Barrow ya kori babban hafsan sojin kasar Gambia

Shugaban Kasar Gambia Adama Barrow ya kori babban hafsan sojin kasar Janar Ousman Badjie, inda ya maye gurbin sa da Janar Masanneh Kinteh, wanda mai bashi shawara na musamman ne kan harkokin soji.

Adama Barrow Shugaban kasar Gambia
Adama Barrow Shugaban kasar Gambia REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Rahotanni sun ce za’a tura Janar Badjie aikin diflomasiya a wata kasar waje, yayin da shugaban kasar ke ci gaba da kakkabe magoya bayan tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh.
Shugaba Barrow ya sha alwashin gudanar da bincike kan zarge zargen cin zarafin jama’a da akayi a karkahsin tsohuwar gwamnatin Jammeh.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.