Isa ga babban shafi
Kamaru

Wata kungiya ta soki katse Intanet a yankunan Kamaru

Kungiyar Internet Without Borders ta ce yanzu haka an kwashe sama da wata guda da katse daukacin hanyoyin sadarwar intanet a Yankunan kasar Kamaru da ke amfani da turancin Ingilishi.

Fiye da wata guda da datse hanyoyin sadarwa na Intanet a yankunan Kamaru da ake turancin Ingilishi
Fiye da wata guda da datse hanyoyin sadarwa na Intanet a yankunan Kamaru da ake turancin Ingilishi
Talla

Julie Owono, lauyar da ke kare kungiyar ta ce wannan shine karo na farko da aka samu irin wannan katsewar, sakamakon zanga zangar da matasa suka yi kan halin da yankin su ke ciki.

Gwamnatin Kamaru ta ce ta dauki matakin ne dan dakile yaduwar labaran da basu da sahihanci da ke kuma haddasa tarzoma a kasar.

Mazauna yankunan da ke turancin Ingilishi wadanda ‘yan tsiraru ne a kasar suna zargin yankunan da ke anfani da Faransanci wadanda suka fi yawa da nuna musu wariya.
 

A baya a wata zanga-zanga da aka yi a garin Baminda da ake turancin Ingilishi kan adawa da gwamnati bisa tilasta anfani da yaren Faransanci a Kotu da makarantu a yankin, mutum guda ya rasa ransa yayin da 'yansanda suka tsare mutane fiye da dari daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.