Lafiya
Masana sun gano nau'in cutar Malaria mai bijirewa magani
Masana kiwon lafiya sun ce a karon farko sun gano wani nau’in cutar malaria dake bijirewa maganin Artemisinin a nahiyar Afrika.
Wallafawa ranar:
Talla
Binciken ya haifar da fargaba kan yiwuwar samun koma baya ga samun nasarar yaki da cutar dake kashe miliyoyin mutane kowacce shekara a nahiyar.
Sakamakon binciken ya nuna cewa, Afirka tabi sahun Asia wajen samun wannan nau’in cutar dake bijirewa maganin.
Kididdiga ta nuna cewa, cutar maleriya ta kama mutane sama da miliyan 200 a shekara ta 2015, yayin da 438,000 suka mutu, kuma mafi yawa daga ciki yara ne kanana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu