Isa ga babban shafi
Nijar

An kai hari wani barikin soja a Nijar

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan wani karamin barikin sojin Jamhuriyar Nijar a kusa da kan iyakar kasar da Mali.Lamarin dai ya faru ne cikin daren laraba, yayin da rahotanni ke cewa an kashe sojojin kasar Nijar akalla 11. 

Shugaban Jamhuriyar Nijar  Issoufou Mahamadou
Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou
Talla

An kai harin ne akan wani karamin barikin soji da ke cikin yankin Ouallam kusa da iyakar Nijar da Mali, barikin da ke karkashen wata babbar bataliyar soji da ke Tilwa kamar dai yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.

Maharan sun afka wa barikin ne a daidai lokacin da rana ke faduwa, bayan sun kashe sojojin 11, sun kuma yi awon gaba da motoci 7 sannan suka kona sauran manyan motoci da kayayyakin da ba za su iya tafiya da su ba.

Daga bisani sai maharan suka doshi bangaren iyakar kasar ta Nijar da Mali, yayin da bayanai ke cewa sai  wayewar gari ne dakarun Nijar suka bi sawun su, tare da sanar da takwarorinsu na kasar Mali da ke yankin Menaka, Asongo da kuma Aderamboukane domin samun dauki.

A watannin da suka gabata an sha samun irin wadannan hare-hare a kan dakarun na Nijar da ke iyaka da Mali, inda aka samu asarar rayukan sojojin kasar da dama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.