Isa ga babban shafi
DR Congo

Congo na fuskantar Matsin lamba kan kisan fararen hula

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo da ta gudanar da bincike kan bidiyon da ke nuna yadda sojoji suka harbe fararen hular da basa dauke da makamai.

DR Congo na fuskantar matsin lamba kan kisan fararen hula a kasar.
DR Congo na fuskantar matsin lamba kan kisan fararen hula a kasar. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Hukumar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar ta bayyana kashe mutane sama da 280 a tashin hankalin da aka samu bara a Yankin Kasai, inda jami’an tsaro suka fafata da ‘yan wata kungiyar da ake kira Kumina Nsapu.

Shugaban hukumar Zeid Ra’ad al Hussein ya ce akwai kwararan shaidun da ke nuna yadda jami’an tsaron ke amfani da karfin da ya wuce kima.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda sojojin suka bude wuta kan fararen hula.

Tuni kasashen Faransa da Amurka suka bukaci gwamnatin DR Congo ta gudanar da bincike kan faifan bidiyo da ke nuna yadda aka harbe fararen hula 50 zuwa 100.

Ma’aikatan harkokin wajen Faransa ta bukaci hukumomin DR Congo da suyi bayani akai da kuma daukar matakan ladabtar da sojojin da suka aikata kisan gillar.

Kasar Amurka ta ce ta damu da hotunan da tagani, inda ta bukaci gudanar da bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.