Isa ga babban shafi
Somalia

Farmajo ya zama sabon shugaban kasar Somalia

Hukumar zaben kasar Somalia ta sanar da tsohon firaministan kasar Mohammed Abdullahi Farmajo a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar.

Mohamed Abdullahi Farmajo sabon shugaban kasar Somalia
Mohamed Abdullahi Farmajo sabon shugaban kasar Somalia REUTERS/Feisal Omar
Talla

Faramajo ya kada shugaban kasa mai ci Hassan Sheikh Mohamud da ya nemi wa’adi na biyu.

A yayin da yake jawabi jim kadan bayan bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar. Mohammed Abdullahi Farmajo ya ce yanzu ne lokacin hadin kan ‘yan kasa tare daukar hanyar yakar mayakan kungiyar Al-shabab da kuma cin hanci da rashawa da yayiwa kasar katutu.

Al’ummar Somalia, da dubban ‘yan kasar da ke tsugune yanzu a sansanin Dadaab na ‘yan gudun hijra mafi girma a duniya, sun yi ta murna da shewa sakamakon nasarar da Farmajo ya samu a zaben.

Farmajo dai ya taba rike mukamin Firaiminista na watanni 8 kacal, a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2011, kafin a sauke shi, sai dai ya jajirce wajen cigaba da fahimtar da al’ummar kasar cewa, shi mutum ne da zai iya kawo cigaba a Somaliya kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen cimma abinda ya sa a gaba.

Babban kalubalen da ke gaban zababben shugaban kasar yanzu shine barazanar tsaron da Somalia ke fuskanta daga mayakan kungiyar Al-Shabab da kuma matsalar cin hanci da rashawa.

An dai kamala zaben na ‘Yan Majalisar dokoki a Somalia cikin tsauraran matakan tsaro har ma da hanawa ‘Yan kasar fita saboda barazanar mayakan na Al Shebaab.

‘yan takara 22 suka nemi kujerar ta shugaban kasa ciki har da shugaba Hassan Sheikh Mohamud da ke neman wa’adin shugabanci na biyu.

Somalia dai ta fada cikin tashin hankali tun bayan kisan da aka yi wa tsohon shugaban kasar marigayi Sa`id Bare a shekarar 1991.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.