Isa ga babban shafi
AU- Morocco

AU ta amince da dawowar Morocco a matsayin mamba

Kungiyar kasashen Afrika ta AU ta amince da bukatar kasar Morocco ta sake zama wakiliya bayan kwashe shekaru 33 da ficewarta daga cikin kungiyar. 

Shugabannin kasashen Afrika a birnin Addis Ababa na Habasha
Shugabannin kasashen Afrika a birnin Addis Ababa na Habasha AFP/Zacharias ABUBEKER
Talla

Bayan kwashe dogon lokaci ana tafka mahawara, wakilan da ke halartar taronsu  a birnin Addis Ababa na Habasha, sun amince su jingine batun yancin Yammacin Sahara zuwa wani lokaci nan gaba, yayin da suka amince da mayar da kasar ta Morocco a matsayin wakiliya.

Kasashen Algeria da Afrika ta Kudu na daga cikin masu adawa da mayar da Morocco cikin kungiyar, har sai ta amince da shirin bai wa yammacin Sahara yancin kai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.