E. Guinea ta tabbatar da bai wa Jammeh Mafaka
Kasar Equatorial Guinea ta sanar da cewar ta bai wa tsohon shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh masauki bayan ficewar sa daga Banjul.
Wallafawa ranar:
Ministan yada labaran kasar Eugenio Nse Obiang ya shaidawa manema labarai cewar Jammeh na kasar ba tare da cikkaken bayani kan halin da yake ciki ba.
Jammeh ya bar Gambia ne a karshen mako sakamakon matsin lamba daga kungiyar kasashen Afirka ta Yamma wadda ta tura dakarun ta Senegal dan tabbatar da cewar tsohon shugaban ya sauka daga mulki bayan kayen da ya sha a zaben da aka gudanar.
Kuma wannan shi ne karon farko da Guinea ke amsa bai wa Jammeh Mafaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu